Koto Ta Dakatar Da Kin Karbar Tsofanfun Kudi Da Zai Gudana 10 Ga Wata

ZANGO MEDIA
0


Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da gamnatin tarayya daga aiwatar da wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin kasar.

A bayan dai CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsoffin takardun 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sake.

Jihohin arewacin ƙasar uku ne dai da suka haɗa da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ƙarar a gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna buƙatar kotun da ta hana Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa'adin.

A hukuncin wucin-gadin da suka suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagaorancin mai shari'a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar sun jingine batun aiwatar da wa'adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin ranar 15 ga watan Fabrairu.

Da wannan hukunci dai yanzu 'yan ƙasar za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ƙasar.

Batun wa'adin amfani da tsoffin kuɗin ƙasar dai ya zama wani batu da ya ɗauki hankula a 'yan kwanakin nan.

Hankulan 'yan ƙasar sun rarrabu game da wa'adin, inda wasu ke ganin ya kamata a ƙara wa'adin, a gefe guda kuma wasu kuma na ganin bai dace a ƙara ba.

Daga cikin waɗanda ke ganin ya kamata a ƙara wa'adin harda ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki, wadda ta gana da shugaban ƙasar a makon da ya gabata kan lamarin.

BBC HAUSA

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)