Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al'ummar ƙasar da safiyar yau Alhamis.
Buhari, wanda ya ce yana sane da irin halin wahala da al'ummar ƙasar ke ciki, ya ce za a ci gaba da amfani da takardar kuɗin ta naira 200 har zuwa 10 ga watan Afrilu.
Ya kuma buƙaci al'umma da su ƙara haƙuri kan halin da ake ciki.
Za mu kawo maku ƙarin bayani kan bayanin shugaban ƙasar.
BBC HAUSA
