Yoyan fitsari wata babban matsalace da ta addabi Mata musanman a karkara ko wasu daidaikun daka birane wanda hankan ya samo asali ne da ka wasu dalilai da suke afkuwa ga mata masu yawa wanda zami bayanin su daya bayan daya
Da fari zamu fara magana akan abubuwan da suke kawo matsalar yoyan fitsari zamu fara duba ga wasu abubuwa guda uku
A.I.G.DALA ZANGO CEMIST
- Doguwar naguda~ wannan ba sabon Abu bane a masaniyar kowa sau da yawa akan sami doguwar naguda game haihuwa wannan shine abu na kan gaba wajan jawo yoyan fitsari ga mata ta dalilin da a lokacin da mace ta samu kanta a wannan yanayi zai zamo a wajan haihuwar ko kugunta matsantsene ko kuma kan yaron yana da girma ma'ana bazai iya fitowa ta sauki ba ko ma gaba daya hakan zai kawo doguwar nakuda, dalilin hankan zai zamo kan jariri zai dinga gogar fatar da take tsakanin mafitsara da gurin harta sami matsalar hujewa fitsari ya dinga fita konace yoyo
- Kaciyar mata~Duk da dai kai ya waye amma har iyau akwai wasu kalilan da suke rike da wannan batarciyar al'ada wanda tana daya daka cikin abin da yake haddasa yoyon fitsari saboda garin yin kaciyar za a ragewa fatar karfi, dan haka wajan haihuwa yaro zaiyi kusa da jakar fitsari ya bata matsala daka nan sai yoyon fitsari
- Kari wajan haihuwa~ wannan yana daya daka dalilan da ake cewa akai mace asibiti danta haihu a hannun kwaranrun ma'aitan ungozoma saboda in karin ya kama su sun san inda zasu taba su kara mace sabanin wanda ba kwaranruba ba sai na zurfafa jawabi anan ba domin kowa yasan in aka hadu da wadda bata da ilimi akan ungozomanci tazo yin kari to yoyo salamu alaikum
Dalilin hakan mata da yawa suna samin kansu a yanayi mara dadi wanda daka karshe wasu mazan sukan guji matan su harma da wasu daka cikin yan'uwaKarkashin haka ya kamata ayi karatun ta nutsu wajan gujewa wannan matsalar
07061658592
