Majalisun Najeriya biyu sun ce suna nan a kan bakansu cewa sai babban bankin ƙasar ya ƙara wa'adin daina amfani da tsoffin takardun naira zuwa watan Yuni.
'Yan majalisar ta wakilai da dattawa, sun ce kwana goma da Babban Bankin ya ƙara sun yi kaɗan, kuma idan aka ci gaba da tafiya a haka mutane da dama za su talauce.
Tun da farko Babban Bankin ya ce tsoffin kuɗin da suka rage a hannun jama'a yanzu, ba su fi kashi 25 cikin 100 ba, kuma cikin kwana goma ana iya mayar da su bankuna.
Sai dai da alama waɗannan bayanai ba su gamsar da majalisun ba.
'Karin kwana 10'
Ahmed Bello Umar, daraktan hada-hadar kuɗi na Babban Bankin ya shaidawa BBC cewa a halin yanzu dai ba su hana kashe tsoffin kudi ba, kawai dai bankuna aka hana su fitar.
Sannan a cewarsa koken da jama'a suka rinka yi ne suka tursasawa shugaban kasa amincewa ko umartar a kara wa'adi da kwana 10.
Ahmed ya kuma shaida cewa yadda tsarin ya ke shi ne daga 1 ga watan Fabarairu zuwa 10 ga watan, ana sa ran jama'a su kammala sauya kudinsu a bankunan.
Sannan sauran kwanaki 7, wato daga 10 ga wata zuwa 17 ga watan Fabarairu, mutum na iya zuwa rassa Babban Banki da ke sassan daban-daban na kasar domin sauya kuɗinsu.
"Abin da mu ke son a gane komai ana yin sa ne saboda al'umma wannan ne dalilin da ya sa aka bijiro da hanyoyin da ake ganin zai saukakawa al'umma.
"Sannan a halin yanzu kashi 60 cikin 100 na sabbin kudaden da ake bukata akwai su, shi yasa aka kara kwanaki 10 wanda tabbas kafin nan kudin su wadata a fadin Najeriya.
"Ba mu isa mu yi komai ko yanke hukunci ba, ba tare da izinin shugana kasa ba, kuma ko a wannan lokaci shi ya bada umarnin a kara wa’adin karban tsoffin kudin," in ji Ahmed Bello
BBC HAUSA
