Alakar South Africa da Kasata Nigeria

ZANGO MEDIA
0
TAƘAITACCEN TARIHIN ALAƘAR NIGERIA DA ƘASAR SOUTH AFRICA

YAKUBU AHMAD YAYA
5/9/2019


Akwai tsohuwar alaƙa tsakanin ƙasar South Africa da Nigeria. Duka ƙasashen sun kasance mambobi a ƙungiyar ƙasashen renon Burtaniya  mai suna "Commonwealth of Nations" da kuma ƙungiyar gamayyar Africa maisuna "African Union".


   Lokacinda tsirarun fararen fata suke mulkin wariyar launin fata "apartheid" a South Africa, Nigeria itace ƙasarda tafi kowace ƙasa a duniya taimakamusu don ganin sun samu cikakken iko a ƙasarsu tareda dakatarda tsarin wariyar launin fata "apartheid" a cikin shirin "anti-apartheid movement" haɗi da ƙungiyar ANC. Gomnatin Nigeria ta samarda Fasfo sama da ɗari uku (300) a mutanen South Africa don sufita ƙasashen duniya don neman ilimi da fafutukar dakatar da mulkin wariyar launin fata da tsirarun farin fata suke musu, a shekara ta 1977, wani mawaƙin Nigeria mai suna Sonny Okasun, ya rubuta waƙa wadda aka mata laƙabi da "Fire in Soweto" domin tinawa da zanga zangar nuna ƙin jinin wariyar launin fata da akayi a garin Soweto a shekara ta 1976 a ƙasar South Africa.


   Bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekara ta 1994 a ƙasar South Africa, ƙasar ta buƙaci ƙwararru a harkokin kasuwanci suyi hijira zuwa ƙasar kuma ƴan Nigeria dayawa sunyi amfani da wannan damar domin fara kasuwanci a ƙasar South Africa. An kiyasta cewa a shekara ta 2011, sama da ƴan Nigeria 24,000 ne suke rayuwa a ƙasar South Africa. Ƙasar ta South Africa ta fara watsi da taimakonda Nigeria ta mata wajen neman ƴanci a hanun tsirarun turawa a lokacinda suka fara zargin ƴan Nigeria da aikata miyagun laifuka a ƙasar tasu. Bugu da ƙari sun zargi ƴan Nigeria da kafa ƙungiya wadda galibi ƙungiyar tanada hannu wajen aikata fataucin miyagun ƙwayoyi wadda sunyi ƙiyasin aikin ƙungiyar ya hauhawa a tsakanin shekara ta 1994 da 1998.


   An cigaba da samun saɓani tsakanin ƙasashen guda biyu a inda a wannan lokacin saɓanin ya ƙazanta sakamakon ƙasar South Africa tanason kifarda tabbataccen shugaba Jean Ping a matsayinsa na Shugaban ƙungiyar gamayyar Africa kuma su musanyashi da ministansu na harkokin cikin gida mai suna Nkosazana Dlamini-Zuma a yayinda itakuma Nigeria take goyon bayan shugabancin Jean Ping. Alaƙa tacigaba da yankewa tsakanin kasashen biyu lokacinda kasar South Africa suka goyi bayan tabbataccen shugaba Laurent Gbagbo don cigaba da mulki marar iyaka a kasar Côte d'Ivoire a shekara ta 2011.


   Duk da haka bayan Dlimi-Zuma tayi nasaran cin zaɓen shugabancin ƙungiyar gamayyar Africa, Ministan harkokin cikin gida na Nigeria, Ambassador Olugbenga Ashiru yace haryanzu Nigeria tana goyon bayan Jean Ping a matsayin tabbataccen shugaban kungiyar gamayyar Africa a inda yake cewa:


   "Wannan shine matakinda yakamata duka mambobin kungiyar ECOWAS su ɗauka kuma muntsaya akai. Amma kamar yadda aka saba, mutane zasu iya tinanin cewa dazarar Nigeria ta ƙauracewa South Africa to hakan zai nuna adawar Nigeria ƙarara akan South Africa. Mu bama adawa da South Africa" a cewarsa.


   Mandela, jagoran ANC na South Africa yayi yunkurin taimakawa don warware rikicin siyasa a Nigeria tun daga shekara ta 1993 biyo bayan soke zaɓen Nigeria a watan yunin 1993. A watan yunin 1994 shugaban mulkin Soja a Nigeria, Janar Sani Abacha ya kama mutane abokan hammayarsa guda 40 tareda yanke musu hukuncin kisa ciki harda Shugaba Olusegun Obasanjo da Chief Moshood Abiola. Mandela ya tura Akbishop Desmond Tutu tareda Mataimakin Shugaban Ƙasa Thabo Mbeki domin dakatarda hukuncin kisan inda sukayi nasarar ceton Obasanjo, Abiola da wasu mutune tara.


   Saidai a yayin taron ƙungiyar Commonwealth na shekara ta 1995 Abacha yasamu nasarar shawokan Mandela inda shi Mandelan ya amince da ƙudirin Abacha na cigabada aiwatarda hukuncin kisa. Baya da haka, ƙasar South Africa ta fara fiskantar cewa alaƙarta da Nigeria yazo karshe a lokacinda Abacha ya kashe Shugabannin Ogoni guda tara ciki harda Ken Saro-Wiwa. A wannan lokacine Shugaba Mandela yayi tofin Alatsine a Janar Abacha akan take haƙƙin bil'Adama wadda hakan ya tilasta kungiyar Commonwealth dakatarda Nigeria a matsayin mambanta har na tsawon shekaru biyu


   Harlau, Mandela ya nemi a dakatarda aikin samarda iskar Gas na kimanin dala biliyan huɗu wadda kamfanin Royal Dutch Shell yakeyi a Nigeria dukda shahararda yayi a Nigeria da sauran sassan duniya


   Wannan yayi sanadiyyar ƙasar South Africa ta keɓance kanta daga harkokin Africa sakamakon tuhumarda akemata na nuna ƙiyayya ga Nigeria.
A tsakanin wata guda ƙasar ta South Africa ta sake yunƙuri dan farfado da dangantakarta da sauran kashashen Africa.


   A ranar 29 ga watan Maris na shakara ta 1995, Wole Soyinka, wadda yakasance jagoran wata ƙungiya mai rajin dimokaradiyya a Nigeria yayi yunƙurin gudanarda taro a kasar South Africa saidai gomnatin ƙasar tayi martani ta hanyar hana Visa ga duk wani mambar ƙungiyar tsawon sati shida (6) kafin taron. Bugu da ƙari jamiyyar ANC mai mulki a kasar ta nemi a dakatar da taron. A wannan lokacinne batun Nigera ya tilastawa ƙasar South Africa shiga sabon tsarin harkokin waje inda shugaba mai mulkin yayi watsi da ware ƙasar South Africa daga harkokin nahiyar Africa a cikin wani sabon shiri da yayi wadda ta nemi ƙulla kawance da kasashen Africa ta hanyar keɓance wasu yanki da nahiyoyi. Hakan ya sanya ƙasar South Africa shiga cikin wani rikici da wasu sassan nahiyar Africa

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)