Ƴan Nigeria sun wayi gari a safiyar 31 ga watan Disamba, 1983 da labarin rushewar jamhuriya ta 2 a Nigeria tare da sabuwar gwamnatin mulkin soja ta tarayya, ta huɗu tun bayan samun ƴancin kai. Birgediya Sani Abacha ne ya sanar da juyin mulkin a gidan radiyon Legas da misalin ƙarfe 8:30 na safe inda ya ayyana juyin mulkin a matsayin kare martabar ƙasa da kuma ceto tattalin arzikin ƙasar daga muyacin hali kuma ya bayyana gwamnatin shugaba Shagari a matsayin gwamnati da take cike da rashawa.
An samu saɓani tsakanin gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari da ɓangaren sojan Najeriya kuma lamarin yayi ƙamari. Babban abin da ya faru shi ne, Janar Muhammadu Buhari, kwamandan runduna ta 3, ya katse man fetur da abinci zuwa maƙwabciyar ƙasar Chadi, matakin da ya haifar da rikicin kan iyaka tsakanin Najeriya da Chadi. Jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, shugaban kasar Shehu Shagari ya nuna rashin amincewarsa da matakin na Janaral Buhari. Buhari ya yi watsi da umarnin da Shagari ya bayar na cewa kada ya shiga ƙasar Chadi, inda rundunarsa ta bi sahun ‘yan ƙasar Chadi kuma suka kutsa cikin ƙasar bayan sun shafe tafiya mai nisan kilomita 50. Wannan lamarin yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka haifar da juyin mulkin, yayin da ya sanya gwamnatin farar hula da sojoji shiga yanayi mai cike da rarrabuwar kawuna
Jim kaɗan gabanin juyin mulkin, babban darakta na Hukumar Tsaro ta Kasa, Umaru Shinkafi, ya gano bayanan sirri da ke da alaƙa da yunƙurin juyin mulkin ta hanyoyi da dama. Duk da haka, Hukumar ta kasa kawar da yunƙurin saboda rashin samun cikakken rohoto kan shirin.
Masu yunƙurin juyin mulkin sun ɗaura wa Kanar Tunde Ogbeha alhakin tattaunawa da jami'an tsaron fadar gwamnati da su miƙa wuya cikin lumana. Ogbeha ya kasa samun Kanal Bello Kaliel wanda shine Kwamandan tawagar sojin da suke kula da fadar shugaban ƙasar, yayin da yayi ta sintiri tsakanin Legas da Abuja don neman ganawa da Kaliel, lamarin ya jefa Kaliel ɗin cikin shakku. Baya da haka, Birgediya Ibrahim Bako shine wanda aka bashi alhakin kama shugaba Shagari bisa tunanin Ogbeha ya yi nasara a tattaunawar miƙa wuya cikin lumana da jami'an tsaron fadar shugaban ƙasar. Saidai kuma Bako bashi da masaniya cewa ba a samu daidaiton tattauna batun miƙa wuya cikin lumana ba. Bugu da ƙari, an fallasa bayanan shirin juyin mulkin a shugaban ƙasa Shagari har ma da Kyaftin Anyogo, sannan kuma Laftanar Kanar Eboma na tawagar sojojin fadar gwamnati ya kai hari da zummar kare fadar shugaban ƙasa. Kamar yadda aka tsara, Birgediya Bako ya isa fadar shugaban ƙasa domin kamo shugaba Shagari amma jami’an tsaron shugaba Shagari ba su miƙa wuya cikin lumana ba kamar yadda aka tsammanta. An yi musayar wuta da ya kai ga kashe Birgediya Bako.
Waɗanda suka shirya juyin mulkin sun haɗa da Manjo Janar Muhammadu Buhari (Kwamandan runduna ta 3, Jos), Moshood Kashimawo Abiola (Hamshakin dan kasuwa wanda ya dauki nauyin yunkurin juyin mulkin a cewar Janar Babangida), Manjo Janar Ibrahim Babangida (Daraktan ayyuka da tsare-tsare na Sojoji), Birgediya Ibrahim Bako (Kwamandan jami'an tsaron fadar shugaban ƙasa), Birgediya Sani Abacha (Kwamandan tankokin yaƙi, tawaga ta 9) Birgediya Tunde Idiagbon (Magatakardan soji), Laftanar Kanar Aliyu Mohammed Gusau (Darektan leken asirin soji), Laftanar Kanar Halilu Akilu, Laftanar Kanar David Mark, Laftanar Kanar Tunde Ogbeha, Manjo Sambo Dasuki (mataimaki kan harkokin soja ga babban hafsan soji, Laftanar-Janar Wushishi), Manjo Abdulmumini Aminu, Manjo Lawan Gwadabe, Manjo Mustapha Jokolo (Babban Malami mai bada horo a barikin Basawa, Zaria) da Manjo Abubakar Umar
Ƙarin bayani: wannan juyin mulkin shine ya kawo Janaral Buhari a matsayin shugaban mulkin soja na ƙasa
Yakubu Ahmad Yaya
02/08/2022