Bakatatan Na Zama Sarki A Kano

ZANGO MEDIA
0
Sanadiyyar Zamana Sarkin Kano – Ado Bayero. Allah yam rahama 

Ina London, sai naji labarin Rasuwar Sarki Inuwa Abbas ALLAH ya Gafarta Masa...

Bayan Kwana 2 sai na sami saƙo daga Premier cewa “In maza in dawo Gida”...

Ban san abinda ake ciki ba, ni a zato na ko wata shawara ce wadda za a yi ta cikin gida.

Saboda haka sai na taho a Jirgin sama, ni ban san dai abinda ake ciki ba...

Sai da na sauka a filin jirgin saman ma da yake ban aikowa kowa cewa ina zuwa ba, sai dai sauka ta daga Jirgin sama, leburori da suke aiki wajensu na fara ji ana “ALLAH Kara maka imani” sai naji kamar mafarki ne, sai na shiga wurin da ake custom, sai naga dai lallai da wani abu, sai naga wani abokina Mr. Abamuche Lawyer.

Daga nan na roƙeShi na nace “don ALLAH a sauke ni gidan commissioner domin ba wanda yasan zanzo kuma ni ban gayawa kowa ba”...

To sai a cikin mota ne nake tambayarsa “kana jin Hausa kaji abinda mutanen nan suke nufi da cewa ALLAH ya ƙara maka Imani”?

Ni kuwa nan gaisuwa ce da ake yiwa Sarki!

Sai yace da ni “ai kaine Sarki” ai anyi maka sarki duk an faɗa a Rediyo an faɗawa Jaridu...

To babu abinda yazo zuciyata alokacin sai tunani na wannan abu mai nauyi da Ubangiji ya ɗora min, ga dai karancin shekaru ga kuma rashin shiri...

Wato rashin shiri sabida ni ban soma da ko hakimta ba wanda za a soma sha’ani da irin wannan na sarautar babbar kujera haka.

Amma kuma wato a wannan lokaci sai na tuna Ubangiji baya ɗorawa mutum kayan da ba zai iya ɗauka ba, kuma na tabbatar Ubangiji mai taimako ne ga bawansa.

Saboda haka sai zuciyata tayi ƙarfi wato sanin in sha ALLAHU Ubangiji na tare da duk mai neman taimako a wajensa...

Kuma na yiwa Allah godiya irin yadda zan iya yi, godiya irin wadda mutum zai iya in bukatarsa ta duniya ta biya. Inji Marigayi Mai Martaba Alhaji Ado Abdullahi Bayero.

Allah ya kyauta makwancin magabatanmu.
A.I.G.DALA

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)