MALLAM IBRAHIM KHALIL: Karka Bari A Zugaka Kayi Rigima Da Kwankwason

ZANGO MEDIA
0
    Mallam Ibrahim Khalil, wanda ya nemi takara gwamna a jam’iyyar ADC, ya shawarci zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da kada ya sake ya bari wasu gurbatattun ƴan siyasa su ziga shi ya yi rigima da mai gidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso.

   Sheikh Khalil, wanda ya zo a na huɗu a zaɓen gwamna daya gabata da akayi ranar Asabar, ya bada wannan shawara ne a wani shiri da yayi a Freedom Radio a Kano ranar  Talata.


   A cewar Sheikh Khalil, Abba Kabir Yusuf ya maida hankali wajen dakile duk wata kofa ko kafa da za  a iya amfani da ita wajen haddasa rigima ko sabani a tsakanin sa da megidan sa Kwankwaso.


  Ya kara da cewa a matsayin sa na ɗan sarauta, wanda kakanninsa suka yi shura wajen hakuri da dattaku, to ya daure ya gaji wannan halin ya yi hakuri da mai gidansa Kwankwaso da yan Kwankwasiyya.


  Ya shawarci Abba da ya sani cewa al’ummar Kano zai mulka ba ƴan Kwankwasiyya ba, inda ya shawarci zaɓaɓɓen gwamnan da ya yi kokari sosai wajen cika alkawuran da ya ɗauka wa mutane a jihar Kar ya nuna banbanci a tsakani ko nuna kabilancin wane ba jam'i yar mu dayaba


  “Kada Abba ya bari a ziga shi ya yi rigima da Kwankwaso. A matsayin sa na ɗan sarauta, wadanda aka sani da sun gaji hakuri, to ya daure ya yi hakuri tsakaninsa da mai gidansa da kuma yan Kwankwasiyya. Sannan ya toshe kunnen sa ga sauran al’ummar jihar tunda dama mulki ya gaji yabo da suka kuma dole ya zama me hakuri.


“Abu na biyu shine, Abba ya yi kokari ya zamana cewa gwamnatin sa gwamnati ce ta al’ummar jihar Kano ba gwamnatin ƴan Kwankwasiyya ba,” in ji Sheikh Khalil.



Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)