Daka cikin wasu masana tarihi sun fada cewa mai yiwuwa an fara ƙirƙirar taliya tun daga karni na 1 Kafin Haihuwar Annabi Isa AS.
Asalin taliya an samota ne daga bangaren Italiyawa, mai yiwuwa ta fito ne daga abincin Larabawa da ake kira "itriyya" a lokacin a karni na 7 AD lokacin da Larabawa suka mamaye Yankin Sicily a Kasar Italy 🇮🇹. A karni na 12 Taliyar Siciliy ta taliya ta zama ruwan dare.
A dangane da wannan Tarihin Kuma ya bayyana cewa Marco Polo ne kawo taliya turai har zuwa Italy lokacin da ya fara kawo ta daga China, Amma alamu sun nuna akwai taliya tun kafin tafiyarsa.
Yayin da masana ke ci gaba da bincike kan ko Sinawa Yan chana ne ko Farisawa ne suka fara yin taliya, abin da muka sani shi ne a kasar Italy ne aka sa mata suna.
Spaghetti ta fara yaduwa ne a Italiya bayan kafa masana'antar spaghetti a karni na 19, wanda ya ba da damar samar da spaghetti mai Yawa don kasuwar Italiya.
Kalmar Spaghetti 🍝
Spaghetti kalma ce ta yaran Italiyanci Wato spaghetto, ma'ana Liyafa
(musamman wanda ake yi wa taron jama'a)
Wanene ya shigo da taliya Afirka?
Taliya bata karaso nahiyar Afirka ba sai da aka kammala yakin duniya na biyu, a lokacin da aka kawo 'Sojjojin Kasar Italy da yawa aka Ajiyesu a kasar Afirka ta Kudu a matsayin fursunonin yaki, kuma ta haka ne aka samu tabbatuwar Al'adun italiyawa da cimakar su ciki har da taliya a Kasar Afrika ta kudu.
Yaushe spaghetti ta zo Najeriya?
(1972)
Spaghetti irinta italiyawa yawanci ana yin ta daga durum Semolina da alkama. Kamfanin Flour Mills of Nigeria Plc ya kafa masana’antar taliya ta farko a Najeriya a shekarar 1972 kuma kira ta da “Golden Penny Pasta”.
Har kawo iyazu da aka samu kanfanoni da dama wanda iyanzu ta karbu a nahiyoyi da dama a duniya
A.I.G.DALA