Tarihin Samowar Jahar Kano

ZANGO MEDIA
0
TARIHIN SAMUWAR JIHAR KANO

   Kano, gari ne mai daɗaɗɗen tarihi, garin da a wannan shekara ta (2020) ya kai kimanin shekaru dubu ɗaya da goma sha Ashirin da daya (999 zuwa 2020). Gari ne da ya fara daga sansanin mafarauta a mafi shaharar ruwayoyi, har ya zama katafaren birni sannan daka bisani ya rikiɗe ya koma masaurauta me karfin gaske, sannan Kuma lardi, daga bisani kuma ya zama jaha a wadda tafi yawan  jama’a a duk faɗin ƙasar Najeriya.


   Wannan jaha daga shekarar da aka ƙirƙire ta zuwa yau, ta samu jagorancin gwamnoni har goma sha bakwai daga shekarar haihuwarta 1967 zuwa 2023


   Akwai gurare masu daɗaɗɗen tarihi a wannan jaha da suka haɗa da duwatsun Dala, Goron Dutse, Magwan, da kuma Dutsen Fanisau. Sannan kuma akwai muhimman gurare da abubuwan tarihi da suka haɗa da ganuwa da ƙofofin gari, gidajen sarauta, da masallatai waɗanda aka giggina tun zamanin sarakunan baya, marina, majema, da sauransu wasu abubuwan tarihin wanda Allah ya albarkaci jahar dasu.


   Kasuwanci da sana’a, na zamani da na tale-tale ma'ana dauri, kai ka ce ba wani gari in ba Kano ba. Sana’o’in ƙira, farauta, fatauci, wanzanci, ɗinki, jima, rini, da sauransu, duk ana yi a Kano tun daga 999 har zuwa 2016. Waɗannan sana’o’i su suka haifar da kasuwannin da suka zama manya a Afirka.


   Tabbas, ba zai yiwu duniya ta manta da Kasuwar Kurmi ba, haka nan Kasuwar Kantin Kwari, Babbar kasuwar kayan amfanin gona ta Dawanau; ƙwarai, wannan kasuwa ta kere duk sa’o’inta a iya faɗin Afirka. Akwai wasu kasuwannin kamar irin su Kasuwar Ujile, Kasuwar Mariri, Kasuwar Ƙofar Wambai, Kasuwar Rimi, Kasuwar Sabon Gari, Kasuwar ‘Yan Lemo, Kasuwar ‘Yankaba, kasuwar kofar ruwa da sauransu. Duk a Kano suke da ma waɗanda ban kawo a wannan rubutun nawa ba saboda Allah ya albakaceta da sana'a da kasuwanci iri-iri musanman da muka tautauna da kakana MALLAM ABBA KASIM DALA saboda dayane daka Wanda suka rage a cikin kwaryar jahar a unguwar Dala Wanda da yayi fatauci tare da sana'ar dukanci Wanda har yanzu yana kan sana'ar tasa ta dukanci 

   Bayan haka akwai tarihi kala daban daban akan asalin wanda ya fara zama a jahar Kano wadda tarihi yafi shihura akansa shine kanoji wanda masana tarihi suke fi bada tarinsa zamu bada tarihin nasa Nan gaba daka inda yake da dalilin zuwansa jahar ta Kano

      MANAZARTA:

   Kano State Ministry of Commerce (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

   Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

    Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

     Yakasai T. (2004). Tanko Yakasai, The Story of a Humble Life

A.I.G.DALA

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)