Hanta wata muhinmiyar gabace da take ciki a dai dai bangaran dama daka sama duk da kasancewar akwai wata tsoka me fadi dake tsakanin ciki da kirji wadda hanta na kasa da ita
Tanada nauyi kimanin na kilogram daya da rabi (1.5kg) hakanan adadin jini yake gudana a duk minti na kowanne awa ma'ana minti daya yakan samarda lita da rabi na jini
Ita take samar da ruwan madaciya dake tarka abinci a jikin kitse har jiki ya sami damar zukar kitse daka karamin hanji zuwa cikin jiki sannan jini ya mikashi zuwa sauran sahsan jiki
Tana kuma aiki wajan kawar da gubar da mutum ya samu ko wasu kwayoyi cuta kama daka kan bakteriya da baros
Itace kan gaba wajan samar da jinin da dantayi ke samu a cikin jikin mahaifiya,da wajan sarrafa anjiyar sinadaran muhimmai kamar vitamin B12 da kuma sinadarin Iron
Hanta ita da saifa suna daukar kwana 120 wajan kashe sinadare raunan jajayen kwayoyin jini bayan kwana 120 cif
Hantace keyin aikin samar da dumi na jiki dan samin lafiyaryiwar rayuwa
Ita take yakar bakin abubuwa da suke biyo abinci su taba lafiya domin tana samar da sinadare da sukewa garkuwar jiki kaimi wajan koran cutuntuka da abinda basu da amfani
Bayan narkawar da ma'aikatar narka abunci keyi hanta ita take karasa aikin narka sinadaran yanda jiki zayi amfani dasu kamar su mai,furotin,bitamin da magunguma
Haka zalika ita take ajiyar abinda yaiwa jiki yawa na sinadare gaba lokacin da jiki yake bukata ya karba
Da yardar Allah gaba zamu kawo alomomin da take nunawa wajan kamuwa da cuta
A.I.G.DALA ZANGO CEMIST
