MATASAN DALA KU KARA DAGEWA
A siyasance tsaffun kurmi sun toshe ko ta ina da matasa zasuyi tasiri a wannan lamari,Daka cikin mu sai dai su zakulo marokansu 'Yanta'addancinsu da kuma 'Yan barandansu sune kadai masu morewa 'yancin cin gashin kai
Banban matakin daya kamata mu dauka mu cinma burin mu shi ne mu janye kanmu daka hayagaga ta guntsi fesa da mafi yawan matasa suke barankadama a ciki saboda a fayintar da nayi cewa ana fafutukar tafiya ne domin kafa tuta a tsakiyar sansani sukuma wasu daka ciki kokawa suke wa zai zauna a gaban mota koda kuwa an basu damar zama a gaban motar tukin ganganci zasuwa al'uma su biya bukatar su su hofantar da masu Kima kaga ke nan tarihi ya maimaita kansa kuma al'amarin ya zama ba alkibila a ciki
A shawarce, hannu daya baya tafi, karfe daya baya amo, karku bari bukatarku tai mutuwar tulun 'Yangaruwa ma'ana anyi asaran tulun gashi ba a sami kudin sai da ruwan ba ga kuma jikewa da akai ma'ana dai batan bakatantan, Ku sani sabon kuturune yake shabune tsohon kuma sai dai gwalo.
Abun daya kamata Ku tashi kuyi kuwa a tare da amo daya yadda muryarku zata zama me anfanar daku in Kuka bari haka zaku ci gaba da rayuwa baku amfanar da junan Ku kome ba, haka zaluka Ga Karin shawara a gareku da yawa wadda ya fito da cikin Ku bakwa bashi goyan baya to Ku sani.
Yada fasihanku yana daukaka kimar yanki Ku domin bajintarsu fitoma take a madadin yanki Ku haka zalika suna dasa sunan yankin a tasahuran duniya domin ako da yaushe gwani yai gwaninta bayan tanbayar sunan sa tambayar daka ina yake ita take biyowa baya
Duba da samin zakakuri a wannan yankin namu dole mu tayashi murna da goyan baya domin Kara daga darajar sa data yankin mu da bashi goyan baya wajan cinma abin da yasa a gaba wato san SANIN BABA
(A.I.G.DALA)