Gwamnan Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano ya musanta labarin da yake yawo na cewa ya kwace lasisin filin shakatawa na Kano club dake cikin garin Kano in da ya sanar kawai shaci fadene na wata gidan jarida. Dan gane da hakan kuma labari yai ta yawo a social media na cewa an cefanar dashi gaba daya Wanda wannan duk kagene.
Jawabin ya fitone ta bakin kwamishinan yada labare na jakar Kano, kwamared Muhammad
Garba cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa, inda yace Wa'adin na bada filin ne ya kare tun a shekaran 2019 amma duk da hakan ba'a kwace ba, sai dai kawai ma'aikatar kasa ya sanar da mamallakan filin karewar Wa'adin su.
Tuni hukumar gudanarwar filin ta kira taron manema labarai ta Kuma sheda musu cewa Wa'adin shekaru 93 ne ba shekara 40 ba kamar yadda ma'aikatar kasa ta bayyana a baya ba
A.I.G.DALA