DEPRESSION:
1. Depression matsalace da take shafar zuciya hadi da kwakwalwa. Mutane da yawa suna gani cewa depression shine mutum ya shiga matsala ko ya rika jin haushi fushi da bacin rai na dan wani lokaci kalilan ko dogon zango. Sai dai depression ya wuce haka. A turance depression yana nufin a danne wani a hanashi rawar gaban hantsi ta ko wane hali. Ko kuma Mutum ya shiga wani yanayi da bature yake cewa 'boredom', wato yanayi na rashin abun yi.
2. Abin da zamuyi zamuyi magana akai shine Clinical depression, ana kuma kiransa da major depressive disorder ko, ko biochemical depression, ko endogenous depression ko biological depression ko kuma unipolar disorder. Duk wadannan sunaye ana amfani dasu wajen kiran irin depression da yake zama matsala ga rayuwar mutum, ta yadda in ba asibiti akaje ba, dai dai abu yayi ta kara gaba.
3. To yaya ake gane cewa mutum yana fama da clinical depression? "International Statistical Classification of Diseases and Related Health Problems 10th Revision (ICD-10)" wata hanya ce da WHO ta samar don gano alamomin ciwuka irin depression. A tsarin ICD-10, ana tabbatar da cewa mutum yana da clinical depression ne idan ya shafe akalla sati biyu dauke da alamomin clinical depression. Sannan kuma sai wadannan alamomi sun zama ana tare dasu kullum ko kuma kusan kullum kafin a kai ga tabbatar da cewa akwai depression. Sannan ba za a tabbatar da clinical depression ba har sai wadannan alamomi (symptoms) sun zama suna kawo matsala ga tsarin rayuwar mai fama da clinical depression, kamar misali suna kawo matsala ga yadda yake gudanar da aikinsa, ko alakarsa da iyalinsa, ko sauran jama'a ko kuma sauran abubuwa masu muhimmanci ga rayuwar mara lafiya. A takaice dai dole matsaloli su zama sun mayar da tsarin rayuwar mara lafiya ya sha bamban da na sauran mutane.
4. Idan aka samu akalla biyar daga cikin wadannan alamomi a tare da mara lafiya to za a tabbatar da cewa mutum yana fama da depression,
a. Baƙin ciki da debewar tsammani a rayuwa (hopelessn)
A.I.G.DALA